Gwamnan Bauchi ya naɗa Haruna Ɗanyaya sarautar Sarkin Ningi na 17

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya naɗa Alhaji Haruna Yunusa Ɗanyaya a matsayin Sarkin Ningi na 17 wanda ke da daraja ta ɗaya.

Cikin wata takarda da mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kwamared Muktar Muhammad Giɗaɗo ya fitar, ya ce sun yi naɗin Sarkin ne ƙarƙashin dokar naɗa sarakuna ta jihar kuma da tantancewa daga Majalisar naɗa sarakuna ta gargajiya ta jihar.

Sakataren gwamnatin Bauchi, Barista Ibrahim Muhammad Kashim ya isar da saƙon naɗin Sarkin cikin wata takarda da ya fitar.

Gwamnatin jihar ta gamsu cewa sabon Sarkin zai ɗora kan ayyukan da mahaifinsa ya bari na ƙoƙarin samar da haɗin-kai, zaman lafiya da ci gaba a Masarautar.

Gwamnan ya kuma yi addu’a ga marigayi tsohon Sarkin Masarautar kan samun rahamar Allah da kuma fatan sabon Sarkin ya kasance cikin ƙoshin lafiya da rayuwa mai ɗorewa a yayin gudanar da ayyukansa.

By Babaji