Gwamnatin Tarayya ta fara ginin gidaje 500 a Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Ma’aikatar gidaje da raya birane ta fara aikin ginin gidaje 500 a Kano.

Rukunin gidajen da a ke kira ‘Sabunta Fata” su na nan a ƙauyen Lambu da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Aikin zai samar da rukukin gidaje masu ɗakuna biyu da masu ɗakuna uku yayin gudanar da aikin.

Ministan gidajen da raya birane Arc Dangiwa ya bayyana haka ne yayin ziyarar gani da ido da ya kai wajen, inda ya nuna rashin jin daɗin shi bi sa yadda aikin ke tafiyar hawainiya.
Ya umarci ɗan kwangilar da ya hanzarta a kan aikin ko kuma a ba wani wanda ya shirya aikin.

A nashi martanin, ɗan kwangilar ya bayyana cewa za su yi aiki sosai, kuma ya bada tabbacin kafin su sa ke dawowa aikin zai yi nisa.

By ukarofi