
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Babban bankin Nijeriya, CBN ya kori baki ɗaya hukumar gudanarwa ta offishin Shirin bada aron Kuɗi ga Manoma na Ƙasa (NIRSAL).
Cikin waɗanda aka tsige akwai Darakta-Manaja kuma shugaban ofishin, Abbas Umar Masanawa; Daraktan ayyuka, Kennedy Nwaruh da Daraktan harkokin gudanarwa, Olatunde Akande.
Wani jami’in NIRSAL ya faɗi hakan inda ya ce gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ta tabbatar da hakan.
Ya ce, yawancin ma’aikatan ofishin sun firgita ga jin hukuncin kasancewar ba su san mai zai biyo baya ba.
Zuwa ranar Litinin ake sa ran samun cikakken bayani game da hukuncin da shugaban bankin ya zartar.
