
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle da shugabannin sojoji su sauya sheƙa zuwa jihar Sakkwato a ƙoƙarinsa na shawo kan matsalolin taɓarɓarewar tsaro a yankin Arewa-maso-Yammacin Nijeriya.
Mista Henshaw Agubike wanda shi ne Darakta labarai kuma jami’in hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Tsaro ya sanar da haka inda ya ce umarnin wani mataki ne na kawo ƙarshen garkuwa da mutane da ta’addanci a yankin da gwamnati ke yi.
Shiyyar Arewa-maso-Yamma ita ce inda ta’addanci ya fi ƙamari a Nijeriya wanda jihohinta huɗu cikin bakwai na daga cikin guda biyar da aka fi samun batutuwan satar mutane a tsakanin watan Yuli na 2023 da Yuni na 2024.
Jihohin da suka fi samun faruwar hakan sune Zamfara, Katsina da Kaduna yayin da Sakkwato ta zo ta biyar bayan Abuja a mataki na huɗu kamar yadda binciken Cibiyar Leƙen Asiri ta SBM ya nuna.
Rahotonni a lokuta da dama sun sha nuna yadda ƴan ta’adda ke cin karensu ba babbaka inda su ke addabar ƙauyuka da karɓe jagorancinsu gami da tirsasa mazauna yankunan biyan su haraji.
A lokacin da ya ke jawabi game da lamarin, Matawalle yace za su sanya ido kan atsayen da jami’ai ke gudanarwa tare da tabbatar da an fatattaki Bello Turji da tawagarsa.
Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa matuƙa kan yadda ayyukan garkuwa da mutane da ta’addanci ke cigaba da ta’azzara musamman a Arewa-maso-Yammacin Nijeriya.
Matawalle ya kuma tabbatar wa al’ummar jihohin da ma yankin baki ɗaya cewa babu wata alama da jami’an tsaro za su ƙyale yayin da suka ƙaddamar da atsayen fatattakar ƴan bindigar.
Kazalika, ya yi kira ga al’ummar yankin su cigaba da zama a ankare tare da bai wa jami’an tsaro haɗin-kai yayin da gwamnatin tarayyar ta ɗauki matakin kare rayukansu da dukiyoyinsu.
