Ƙungiyar nan ta SERAP ta maka jagorancin majalisun Nijeriya kotu a kan tuhumar ƙayyade ƙuɗaɗen ƴan majalisa.
Waɗanda a ke ƙaran su ne Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kuma Sipika Majalisar Tarayya Hon Tajuddeen Abbas.
Ƙungiyar ta yi kira da cewa jagororin biyu sun gaza wajen hana majalisun ƙayyade ƙuɗaɗen su da kan su.
Mataimakin daraktan a ƙungiyar Kolawole Oluwadare ya bayyana cewa an shigar da ƙarar ranar juma’ar da ta gudana a babbar kotun da ke Abuja. Ya ce wannan ya biyo bayan zargin da tsohon shugaban ƙasa Oluseguj Obasanjo ya yi a makonnin da suka shuɗe in da ya ce ƴan majalisun su ne ke ƙayyade ma kansu ƙuɗaɗen da za su rinƙa biyan kansu ba hukumar RMAFC ba.
