
Daga BELLO A. BABAJI
Jamhuriyar Nijar ta amince ta shiga tawagar tsarin sojojin haɗaka (MNJTF) bayan tattaunawa tsakanin shugaban Ma’aikatan Tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa da takwaransa na Nijar, Janar Moussa Salaou Barmou a Niamey, babban birnin Nijar.
Rahotanni sun bayyana cewa, Janar Musa ya ziyarci ƙasar Nijar ne a ranar 28 ga watan Agusta don haɗe kai da sojojin ƙasar wajen shawo kan matsalolin rashin tsaro da ayyuka masu kama da haka a yammacin Afirka.
Daraktan yaɗa labarai na Hedikwatar Tsaro, Burgediya Janar Tukur Gusau ya ce an cimma ƙulla yarjejeniya ta MOU don inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, a ƙoƙarinsu na magance matsalolin tsaron da suka addabi ƙasashen biyu.
Haka nan, ƙasashen sun tabbatar da cigaba da ƙoƙarin samar zaman lafiya da tsaro da kuma jaddada maƙoftaka ta gari a tsakanin su.
A lokacin da ya ke jawabi, Janar Barmou ya ce a shirye Nijar ta ke ta shiga cikin MNJTF don maslahar Nijeriya da Nijar.
Sakamakon zaman ya kuma ya nuna cewa, za’a samar da kwamitin mashawarta da za su mayar da hankali wajen bunƙasa matakai da suka alƙanta ƙasashen biyu.
