A cikin wani yunƙuri da gwamnati ke yi don ganin a samu wadatattun muhalli, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da bikin ginin sabbin rukunin gidaje guda 1500 a unguwar Rimi da ke ƙaramar hukumar Tofa a Jihar Kano.
Wannan ya biyo bayan yunƙurin gwamnatin wajen ganin faɗaɗa shirin wasu rukunin gidajen guda 500 a ƙauyen Lambu duk a cikin ƙaramar hukumar ta Tofa.
Rukunin gidajen na sabunta fata suna cikin jadawalin Gwamnatin Tarayya na ganin an gina sabbin birane a faɗin ƙasar da ya haɗa da jihohi kamar su Kano, Enugu,Maiduguri, Legas, Fatakwal da Nasarawa.
Yayin wata ziyarar aiki da ministan muhallin ya kai wajen, ya bayyana cewa Shugaba ƙasa da kanshi zai zo ya ƙaddamar da wannan aikin gidajen nan bada jimawa ba.
Ministan ya cigaba da cewa ginin gidajen 500 a Lambu wannan gwamnatin tarayya ce za ta ɗauki nauyin aiki alhali kuma sauran gidajen Unguwar Rimi haɗaka ce tsakanin gwamnati da ƴan kasuwa domin ba ƴan kasuwa zuba hannun jari a cikin aikin.
