APC ta lashe zaɓukan ciyamomi 21 da kansiloli gabaɗaya a Kebbi

Spread the love

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kebbi a ranar Lahadi, ta bayyana jam’iyyar All Progressives Congress(APC) a matsayin wadda ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar a jihar.

Shugaban Hukumar, Aliyu Muhammad-Mera, wanda ya bayyana hakan a Birnin Kebbi ranar Lahadi, ya ce jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun Shugabanci 21 da Kansiloli 225.

Muhammad-Mera ya ce jam’iyyun siyasa 17 ne suka shiga zaɓen da suka haɗa da, APC, NNPP, LP, AAC, Boot party, AP, SDP da dai sauransu.

Sai dai jam’iyyar PDP ta fice daga zaɓen in da tai zargin cewa shugabannin hukumar zaɓen jihar yan jam’iyyar APC ne.

By ukarofi