
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya magantu kan rahotannin da wasu jaridu ke yaɗawa na cewa ya na fama da matsalolin bashi ga masu raba masa man fetur.
Babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Olufemi Soneye cikin wani saƙo da ya fitar a ranar Lahadi ya ce matsalar kuɗin ya sanya kamfanin a halin tsaka-mai-wuya wanda hakan ya sabbaba rashin raba isasshen man fetur kamar yadda aka saba.
Ya ce, la’akari da dokar masana’antar man fetur (PIA), NNPCL zai cigaba da kasancewa madogara ta ƙarshe wajen samar da man fetur don tabbatar da ɗorewa a ɓangaren.
Ya ƙara da cewa, su na aikin tuƙuru da hukumomin gwamnati da lamarin ya shafa don cigaba da raba isasshen man fetur a dukkan faɗin Nijeriya kamar yadda aka saba.
