
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Ƴan kishin Ƙasa ta COPAN ƙarƙashin jagorancin Barista Uchenna Odielli ta yi alla-wadai da yunƙurin da wani ɗan Burtaniya mai suna Andrew Wynne Povich da aka sani da Free Povey ya yi na kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Bayan zurfin bincike da ƴan sanda suka yi, sun shelanta neman sa ruwa a jallo kan ɗaukar nauyin wasu mutane a Nijeriya don nakasa ƙasar ta hanyar haddasa tashin-tashina, zanga-zanga da makamantansu.
Cikin wata takarda da COPAN ta fitar a ranar Litinin, ta ce duk wani yunƙuri na kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin da aka kafa daga ƴan ƙasar waje, abun a yi tir ne da shi.
Ta ce, hakan karya dokar ƙai’dar cin gashin kan ƙasa ne da saɓa wa dokokin demokraɗiyya da na ƙasa-da-ƙasa.
Ta kuma yi kira ga ƴan ƙasashen waje da ke zaune a Nijeriya su girmama zaɓin demokraɗiyya da takwarorinsu suke akai da kuma ƙaurace wa ayyukan da suka shafi maƙarƙashiya.
Kazalika, ta buƙaci ƴan Nijeriya su kasance masu lura tare da bai wa gwamnati goyon baya yayin da ta ke ƙoƙarin magance matsalolin matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar.
