
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Labarai da Haɗin-kan Ƙasa, Idris Mohammed zai wakilci Shugaba Bola Tinubu a matsayin jagoran tawagar Nijeriya a taron ƙasar Indonesiya na Afirka karo na biyu wanda za a yi a Bali daga ranar 1 zuwa uku ga watan Satumba, 2024.
Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce za a yi taron ne don ƙarfafa ayyukan da Indonesiya ke son cimmawa zuwa shekarar 2045 da kuma na Afirka a 2063.
Ya ce, akwai kyakkyawar fahimta da alaƙa mai ƙarfi a tsakanin Nijeriya da Indonesiya inda gwamnatin ƙasar ta bai wa Nijeriya matsayin cibiyar zuba hannun-jari ta Afirka daga 2022 zuwa 2026.
Hakan nan, taron zai taimaka wajen bunƙasa hanyoyin haɓaka tattalin arziƙin Nijeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Indonesiya ta kuma bada tallafin Dala miliyan 2 ga cutuka da riga-kafi musamman ga kula da lafiyar ƙananan yara.
