Sojoji sun kashe shahararren ɗan ta’adda da mutanensa a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ɓangaren jami’ai na musamman sun yi nasarar kashe sanannen ɗan ta’adda mai suna Mustapha Abdullahi da wasu mambobin tawagarsa guda biyar a ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, AVM Edward Gabkwet acikin wata sanarwa da ya fitar yace, an tura jami’an ne daga rundunar kariya ta 413.

Ya ce, an samu nasarar ne sakamakon wani rahoton sirri da suka samu a ranar 31 ga watan Agusta kan cewa an ga ɗan ta’addan da tawagarsa a yankin dajin Sabon Gida, kan hanyar Sabon Birni.

Sun zo yankin ne akan baburansu inda ake zargin su da nufin garkuwa ko cutar da mutane inda suka farmaki rundunar sojojin da ke yankin, akan haka ne jami’an na musamman suka gaggauta buɗe mu su wuta tare da kashe baki ɗaya tawagar ƴan ta’addan.

By Babaji