Matsalolin Nijeriya na buƙatar a yi musu taron dangi, inji Shettima

Spread the love


Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙara jaddada buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin gwamnati da abokan hulɗarta da sauran masu ruwa da tsaki don kawar da talauci da inganta rayuwa ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya.

Shettima, ya faɗi hakan ne a wajen taron majalisar tattalin arzikin Ƙasa karo na 144 a Abuja, inda ya jaddada cewa, samar da yanayin da kowane ɗan Nijeriya ke da damar ci gaba, abu ne da ke ɓukatar haɗin kai.

Sanatan ya yaba da gudunmawar da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gidauniyar Bill & Melinda Gates da kuma rukunin kamfanonin Ɗangote su ke bayarwa wajen gina ci gaban Nijeriya a fannonin da suka shafi lafiya, abinci mai gina jiki, noma, da ilimi.

Taron na NEC ya kuma tattauna kan dabarun da za a bi don magance matsalar ambaliyar ruwa, da rashin abinci mai gina jiki, sannan da yadda za a samar da ‘yan sandan jihohi da maganin cutar shan inna, ciki kuwa har da buƙatar a aiwatar da shawarwarin da aka amince da su a kwamitin wucin-gadi kan ambaliyar ruwa, zaizayar Ƙasa, fari da kwararowar hamada, kana da kafa kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya, da kuma kawar da Cutar Polio.

By ukarofi