Za a ƙara alawus ɗin masu hidimar ƙasa nan ba da jimawa ba – Birgediya Yusha’u

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Babban daraktan hukumar yi wa ƙasa hidima (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa ƙasa hidima cewa za a ƙara musu alawus alawus na wata da zarar ma’aikatan gwamnati suka fara karɓar sabon mafi ƙarancin albashin da aka amince da shi.

A cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NYSC, Caroline Embu, Birgediya Janar Ahmed ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya ke jawabi ga masu hidimtawa ƙasa a sansanin Jihar Kebbi da ke Ɗakingari da kuma sansanin hukumar da ke Jihar Sokoto a Wamakko.

Ya kuma buƙaci masu hidimar da su kasance masu haƙuri da kuma ci gaba da bayar da gudunmawa mai tsoka ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin ƙasa, yana mai jaddada cewa an yaba da ƙoƙarin da suke yi.

By ukarofi