
Daga BELLO A. BABAJI
Aƙalla kwanaki 334 kenan da ƙasar Isra’ila da taimakon Amurka ke yaƙar al’ummar Palestinu wanda hakan ta kai ga neman agaji daga ƙasashen duniya.
A halin da ake ciki, Isra’ila ta na nuna wa duniya irin kisan kiyashin da ta ke yi wa ƴan Palestinu tare da juya baya ga dokokin ƙasa-da-ƙasa.
Wata takarda da ofishin jakadancin Palestinu ya fitar ƙarƙashin jagorancin Abdullah M. Abu Shawesh, ta ce zuwa ranar Talata da ta gabata, adadin mace-mace ya kai 40,738 yayin da na waɗanda suka samu raunuka kuma ya kai 94,154. Haka kuma dubunnai sun ɓata wanda galibin su mata ne da yara.
Ta kuma ce, daga wata Oktoban shekarar da ta gabata, ƴan Palestinu da aka tsare sun kai mutum 10,400 daga yankin West Bank ciki har da ƴara 725, mata 400 da ƴan jarida 98 wanda acikin su, mutane sama da 60 ne suka rasa rayukansu musamman saboda rashin kulawa.
Wannan ita ce shekara ta biyu da ɗalibai ba su samu damar yin karatu ba inda aka tarwatsa makarantu da dama sakamakon cigaba da buɗe ma yankunan ƙasar da dama wuta.
Abu Shawesh ya ce, su na kira ga taron ƙasashen duniya su tsayu wajen tabbatar da zartar da dokar ƙasa-da-ƙasa da tsarin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da sanya harkokin siyasa, tattali da tsare-tsaren difulomasiyya a inda suka dace, da kuma dakatar da zubar da jini da abin da suka kira da ‘American-Israeli carnage’.
