Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta bayar da wakilci na kyauta ga masu zanga-zangar #EndBadGoɓernance da ke da shari’a a faɗin ƙasar.
News Point Nigeria ta ruwaito cewa shugaban NBA, Afam Osigwe, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na ɗ ranar Laraba, ya kuma umurci rassan NBA da su sanya ido kan shari’ar da ake yi wa masu zanga-zanga a faɗin ƙasar.
Ya ce, “Na umurci rassan ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya da su sanya ido a kan shari’ar masu zanga-zangar #EndBadGoɓernance.
“Bugu da ƙari, na ƙaddamar da shirin tallafa wa masu zanga-zangar da ba su da wakilcin doka.
“Ƙungiyar Lauyoyin ‘Yancin Jama’a ta Nijeriya (NBA-CLC) an ɗorawa alhakin tuntuɓar shugabannin da kwamitocin kare haƙƙin ɗan Adam na rassan NBA a yankunan da ake tuhumar masu zanga-zangar a halin yanzu. Wannan yana tabbatar da cewa babu wanda ake tuhuma da zai fuskanci rashin adalci.
“Tawagar lauyoyin NBA za su ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da shari’ar a kotu domin tabbatar da cewa an gudanar da shari’ar tare da bin ƙa’ida, tare da kare haƙƙin doka na duk wanda ake tuhuma.
“Ƙungiyoyin lauyoyin na Nijeriya na cikin kotuna kuma za su ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da shari’a don tabbatar da cewa an bi doka da oda, an kare haƙƙin waɗanda ake tuhuma da kuma tabbatar da adalci.”
An tsare tara daga cikin masu zanga-zangar #EndBadGoɓernance a gidan gyaran hali na Kuje bayan an tuhume su da laifin cin amanar ƙasa yayin da kotu ta bayar da umarnin a tsare mace ɗaya tilo a cikinsu a gidan gyaran hali na Suleja.
Masu zanga-zangar, tare da dubban wasu, sun yi zanga-zangar adawa da yunwa da rashin shugabanci daga ranar 1 zuwa 10 ga Agusta, 2024.
