
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai sanya hannu kan batun ƙarin wa’adi ga Sufeto-Janar, Kayode Egbetokun ba.
Cigaba da aikin shugaban rundunar ya haifar da cecekuce a tsakanin al’umma.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar, rundunar ta ce, madadin haka Shugaba Tinubu ya tsayu ne akan dokar tsarin wa’adin ofishin.
Hakan na zuwa ne bayan da Egbetokun ya cika shekaru 60 a duniya a ranar 4 ga Satumba wanda hakan shi ne matakin ajiye aiki ga ma’aikaci a ka’ida.
Rashin ajiye aikin nasa ya sa al’umma ke tunanin cewa Shugaba Tinubu ya ƙara masa wa’adi ne duk da cewa akwai ƙudirin sauya ƙa’idar wa’adin ajiye aiki da ba a kai ga sanya wa hannu ba.
Adejobi ya ce, takardar ɗaukar aikin Sufeton ya fara ne a ranar 3 ga watan Nuwamban 2023 wanda ta ba shi damar yin shekaru huɗu a naɗin da aka yi masa kamar yadda dokar ƙasa na sakin layi na 215(a) da na 28(c) suka tabbatar.
