Jihohi 21 za su fuskanci ambaliya nan da kwana 5, inji Ma’aikatar Kula da Muhalli

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta aika da saƙon gargaɗi ga al’umma kan mamakon ruwan sama da za a fuskanta na tsawon kwanaki biyar masu zuwa waɗanda hakan ka iya haifar da ambaliya a jihohi guda 21.

Cibiyar aika Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa ƙarƙashin Ma’aikatar Kula da Muhalli ta bayyana haka a ranar Alhamis inda ta ce ana tsammanin hakan ya kasance daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumba.

Ta yi hasashen ruwan saman zai iya sa a samu ambaliya a wurare 123 cikin jihohin da aka lissafa.

Ta kuma bada shawara ga al’umma da ke garuruwan kusa da ruwan ‘River Benue’ su gaggauta barin yankunan saboda akwai yiwuwar a samu ambaliya.

Jihohin da ake tsammanin samun ambaliya sune; Adamawa, Benue, Bauchi, Kogi, Borno, Nasarawa, Gombe, Kwara, Jigawa, Oyo, Kaduna, Edo, Kano, Katsina, Kebb, Plateau, Neja, Sakkwato, Taraba, Yobe da kuma Zamfara.

Hukumomi sun yi kira ga al’umma su kasance masu lura da kuma ɗaukar matakan kariya ga rayuka da dukiyoyinsu.

By Babaji