
Daga BELLO A BABAJI
Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ce yanayin hada-hadar kasuwar duniya na da tasiri wajen sauye-sauyen farashin man fetur wanda ya na tafiya ne da juyawar kasuwanni kamar yadda dokar masana’antar man fetur, PIA ta tabbatar.
Mataimakin shugaban Hukumar Tace Ɗanyen Man fetur na NNPCL, Adedapo Segun ya yi bayanin dalilin ƙarancin man fetur acikin al’umma, ya na mai cewa nan da ƴan kwanaki matsalar za ta kau inda tuni wasu gidajen mai suka fara sayerwa.
Ya ce , sakin-layi na 205 na PIA wanda shi ya bada damar samar da NNPCL, ya ce ana saka farashin mai ne dogaro da yadda tsarin ‘unrestricted free market forces’ ya nuna.
Haka kuma kasuwar shunku, wacce ita ma ta na bada gudunmawa wajen ƙayyade farashin litar man fetur a Nijeriya kan hauhawa ko saukar sa.
Game da batun fara ɗakko man fetur daga matatar Ɗangote, Segun ya ce NNPCL na jiran 15 ga watan Satumba wanda shi ne lokacin da matatar ta bayar.
Ya ƙara da cewa, su na cigaba da aiki da hukumomin da lamarin ya shafa wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar rashin isasshen man fetur a gidajen mansu.
