Mai magana da yawun shugaban ƙasa Ajuri Ngelale ya ajiye aikin sa yau a bisa dalilai na rashin lafiya.
A rahoton da jaridar Blueprint Manhaja ta samu ta tabbatar da faruwan haka duba da yadda labarin ya ke ta yawo a kafafen sadarwa.
Takardar ta bayyana cewa Ajuri ya miƙa takardar ajiye aikinsa na ɗan wani lokaci domin dalilin rashin lafiya da iyalansa ke fama dashi.
Ya bayyana lamarin a matsayin wata damuwa da ta ke hanashi aikinsa yadda yakamata, don haka dole ya ajiye aikinsa domin ba matsalar cikakken kulawa da ya dace.
Daga ƙarshe ya nemi, a mutane su mutunta sirrin shi da na iyalansa domin ganin ya shawo kan wannan lamari.
