An ƙaddamar da kwamitin zakka da waƙafi a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da kwamitin Zakka da waƙafi na gundumomi da na ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.

Ya ce, aikin kwamitin shine tattarawa da raba Zakka da waƙafi kaɗai da ya bayyana ga masu biya a matsayin hanya tabbatacciya ta samun rahamar Allah da shawo kan matsalolin rayuwa.

Acewarsa, ƴan kwamitin sun haɗa da hakimin gunduma da daraktan ilimi da walwalan jama’a a matsayin shugaba da sakatare na kwamitin.

Sauran mambobin sun haɗa da wakilai daga majalisar dokoki, ƴan kasuwa, manoma da ƙungiyoyin Izala da Ɗariƙa a kowacce gunduma.

Gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na yaƙi da munanan ɗabi’u ta hanyar kafa hukumar Hisbah.

A nasa jawabin shugaban hukumar Zakka da waƙafi na jihar, Dakta Ahmad Musa Filin Sami ya bayyana cewa, hukumar ta ƙudiri aniyar karba Zakka da waƙafi da zai kai kuɗi Naira biliyan 3.5.

Ya faɗa cewa, hukumar ta gano mabuƙata su 5,000 a ƙaramar hukumar da zasu amfana da Zakka.

By Babaji