Kannywood rashin jini rashin tsagawa ce – Galadima Muhammad 

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Muhammad Galadima shi ne wanda ya kula da shirin fim ɗin ‘Kuka Bulukiya’, wanda ya samu karramawa a taron Nigeria Week da aka gudanar a birnin Landon.

Blueprint Manhaja ta tambaye shi yadda ya ji da ya samu labarin fim ɗin ‘Kuka Bulukiya’ ya yi nasara, sannan ko me labarin ya ƙunsa da kuma saƙon da fim ɗin ya ke isarwa?

Sai ya ce, “To shi wannan fim ɗin na ‘Kuka Bulukiya’, ni na kasance a matsayin mai wakiltar furodusa, kuma mai kula da wajen shirya fim ɗin, sannan kuma ni na kasance a matsayin mataimakin darakta, haka nan kula da walwalar ma’aikata dukka dai a hannuna abin yake, wanda zan iya cewa ni ne ƙashin bayan aikin idan ka ɗauke babban furodusa.

Kuma shi wannan aikin fim ɗin an yi shi a matsayin da an tafi za a yi shi a matsayin gajeren fim. Sai kuma da aka je aikin sai babban furodusan ya mayar da shi mai godon zango, amma duk da haka sai da ya kai kamar kusan sa’a guda.

Kuma shi wannan fim ɗin na ‘Kuka Bulukiya’ labari ne wanda aka yi shi a kan jita da ake yi a kan an taɓa yin wata da ake cewa ‘Bulukiya’, to kuma sai aka ga cewa akwai irin waɗannan mutanen a can baya, ba wai lallai matsafa ba ne, masu bada magani ne, da suke bayar da magani na cututtuka a lokacin. To sai ya zama akwai mutanen da ba su yarda da tsarin ba, saboda sai mutum ya je wajen malami da sauransu haka wanda shi ya fi yarda da shi kenan. Wannan shi ne abin da aka nuna a cikin fim din kenan.”

Ya ci gaba da cewa” Kuma magana ta gaskiya lokacin da muka yi magana da shi babban furodusa ya tafi Landan zai je za a ba shi kyautar karramawa, sai ya kira ni ya ce an shigar da fim ɗin ‘Kuka Bulukiya’ za a kalla, to ban yi mamaki ba. 

Amma gaskiya na yi mamaki da ya kira ni ya ce fim ɗin ya samu nasara. Sannan kuma ya kira ni ya ƙara cewa Kamfanin Moɓing Image Limited, ya sake cin Award, to ka ga wannan abin alfahari ne a ce fim ya samu Award, kuma kamfanin da ya shirya shi ma ya samu Award ai abin murna ne. Domin hakan ya nuna cewar ita Kannywood ɗin nan da ake faɗa, rashin jini rashin tsagawa ce. Idan har za mu ci gaba da jajircewa, to lallai finafinan mu za su je su ci gaba da taka rawa a gurare da dama. Saboda labarin ‘Kuka Bulukiya’, shi kaɗai ne labarin da aka ce a wajen mutane sun ce abin da ya burge su kenan, ko ba ka jin yaren fim ɗin za ka gane Ina labarin ya dosa, don haka duk wani labarin fim mai kyau ya kamata ya zama haka.

Kuma gaskiya mu ne muke raina kanmu a harkar fim, domin shi fim idan ya tsaru babu ruwan sa da addini ko yare da al’ada. Mutane za su so su ga abin da ba su saba gani ba ne. Kuma kullum abin da muke ta faɗa kenan, muna da al’adunmu masu kyau, muna da labarai masu kyau da inganci wanda ya kamata a ce mun yi nisa, amma saboda ba za mu iya jajircewa ba, ko gaggawa, ko wani abu na rashin kuɗi, da kuma mutum ya dage ya ce shi kaɗai zai yi. To duk waɗannan abubuwan su ne suke haifar mana da abubuwa na koma baya a cikin harkar fim ɗin da muke yi. Muna fatan hakan ya zama ƙalubale ga masu kallon ba za mu iya ba.”

By ukarofi