Wike ya gargaɗi gwamnoni su daina tsoma baki a harkokin PDP a Ribas

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin haifar da rikicin siyasa a jihar, ya kuma gargaɗi duk wani gwamna aka da ka da ya yi yunƙurin yin katsalandan a harkokin jam’iyyar PDP a jihar Ribas.

Wike ya bayyana haka ne a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Fatakwal a ranar Asabar a yayin taron jam’iyyar na jihar.

“Bari na tabbatar muku, ba yayin da muke raye ba wani zai ƙwace mana tsarin PDP. Amma bari in gaya wa mutane, na ji wasu gwamnonin suna cewa za su karɓe tsarin su mayar wa wani, ina tausayin waɗannan gwamnonin domin zan kunna wuta a jihohinsu.

“Lokacin da Allah ya ba ku zaman lafiya, kun ce ba ku son zaman lafiya – duk abin da kuka gani ku ɗauka,” in ji Wike.

ƙungiyar gwamnonin PDP a cikin wata sanarwa da shugabanta, Gwamna Bala Mohammed ya karanta a ranar 23 ga watan Agusta, sun jaddada goyon bayansu ga Gwamna Siminalayi Fubara.

Sun yi kira da a sake duba sakamakon taron jam’iyyar don dawo da martabar Fubara a jihar.

“ƙungiyar ta lura da rikicin siyasa a jihar Ribas inda ake amfani da hukunce-hukuncen kotu don tantance sakamakon taron jam’iyyar.

“ƙungiyar Gwamnonin PDP ta sake jaddada matsayarta da Gwamnan Jihar Ribas, kuma za ta tuntuɓi Kwamitin NWC ta babbar jam’iyyar mu don sake ziyartar taron da nufin gyara matsalar da kuma bai wa mai girma Gwamna Siminalayi Fubara damar ya karɓi muƙaminsa na shugabancin jam’iyyar a jihar, “in ji sanarwar a wani ɓangare.

Jam’iyyar PDP a jihar Ribas dai ta shiga cikin rikici ne sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin Wike da magajinsa Fubara.

Gwamna Fubara bai halarci taron na ranar Asabar da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke titin Aba, Fatakwal ba.

Cikin waɗanda suka halarci taron tare da ministan babban birnin tarayya akwai wasu ‘yan majalisa masu riƙe da muƙamai a matakin tarayya da na jihohi, da tsaffin shugabannin kansiloli, da sauran amintattun jam’iyyar.

Kwamishinan zaɓe na INEC da wasu ma’aikatan hukumar suma sun halarci wajen.

By ukarofi