APC shiyyar Arewa ta Tsakiya ta yi Allah wadai da Gwamna Sule kan amincewa da Ganduje

Spread the love

Daga SANI AHMAD GWA a Abuja

Kungiyar Gwamnonin APC ta Arewa ta Tsakiya ta yi Allah wadai da amincewa da Shugaban Jam’iyyar na ƙasa Abdullahi Ganduje da shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa ta tsakiya kuma gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi.

Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar taron da ke Jos babban birnin Jihar Filato, Shugaban ƙungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, ya ce ziyarar ban girma da Sule ya kai wa sakatariyar jam’iyyar a Abuja ranar Juma’a domin ya nuna goyon bayan Ganduje don son kai da son rai ba wll ba wai muradin yankin Arewa ta tsakiya ba, APC ko kuma Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jagoranci gwamnatin.

Shugaban ya ce irin wannan goyon bayan da Gwamna Sule ya yi wanda ke zuwa a lokacin da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga yankin ke ƙoƙarin ganin an dawo da kujerar Shugabancin ƙasa zuwa yankin Arewa ta Tsakiya ba kawai rashin hankali da ɓarna ba ne, har ma da cin amanar yankin bakiɗaya.

Zazzaga wanda kuma mamba ne a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata, ya yi nuni da cewa gwamna Sule ya sani sarai cewa muƙamin shugabancin ƙasa bisa tsarin jam’iyya da shiyya ya kamata ya kasance na yankin Arewa ta tsakiya bayan murabus ɗin Abdullahi Adamu, wanda ba wai daga yankin Arewa ta tsakiya kaɗai ba har ma daga jihar Nasarawa ta Gwamna Sule.

Ya ce Gwamna Sule ya fito fili ya ci amanar jiharsa kuma ɗaukacin yankin ya nuna cewa shi mutum ne wanda baya son ci gaban jiharsa ta Arewa ta Tsakiya, kuma ba mutum ba ne mai adalci da riƙon amana.

“Gwamna Sule ba da shi aka kafa jam’iyyar APC ba, domin ya shigo ne a kan layi, don haka bai fahimci aƙida da ci gaban jam’iyyar ba.

“Don haka ne ya ke yin abubuwan da suka saɓa wa ra’ayin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, manyan sarakuna, jiga-jigan jam’iyya da ‘yan uwa, da kuma magoya bayansa.

“Baya ga dukkanmu mun san cewa a zaɓen 2023, jam’iyyar APC a jihar Nasarawa ba ta yi nasara ba a ƙarƙashin Gwamna Sule; wannan a bayyane yake a yawan ‘yan majalisar da jam’iyyar ta samu da kuma waɗanda jam’iyyun adawa suka yi ta lalube.

“Sannan kuma sanannen abu ne cewa Gwamna Sule ma bai taka rawar gani ba a zaɓen 2023, kuma idan ba ɓangaren shari’a da suka tabbatar da zaɓen sa ba, komai zai iya faruwa kuma da APC ta faɗi jihar.

“Gaskiya mene ne gudunmawar Gwamna Sule ga ci gaban jam’iyyar APC tun da ya koma jam’iyyar? Har ila yau, mene ne irin ci gaban da ya samu a Jihar Nasarawa? Da ƙarin kason da jihohi suka samu a yau, me jihar Nasarawa ta iya yi ko kuma ta nuna a ƙarƙashin Gwamna Sule?

“Kuma a lokuta da dama, mun yi ta kokawa a ɓangarori da dama game da salon jagorancin Gwamna Sule a jihar wanda da yawa suka yi ta raɗe-raɗin.

By ukarofi