Tinubu ya martaba ɗalibai 462 da aka yaye a makarantar kwalejin horo ta ƴan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban ƙasa kuma Kwamandan rundunar tsaro, Bola Ahmed Tinubu GCFR ya tabbatar da yaye ɗalibai 462 daga makarantar kwalejin horo ta ƴan sanda da ke Wudil a Jihar Kano zuwa sahun rundunar ƴan sandan Nijeriya.

Bayan kammala shekaru biyar a makarantar su na karɓar horon karatu da na aikin ƴan sanda, an bai wa kowannen su muƙamin Mataimakin Sufuritandan ƴan sanda (ASPs).

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda, Olumuyiwa Adejobi ya ce an gudanar da bikin yaye ɗaliban ne a filin fareti na makarantar inda masu alfarma daga ɓangarori daban-daban a Nijeriya suka halarta.

An samar da tsarin ne don ba su horon aikin ɗan sanda na zamani tare da kiyaye doka da oda a yayin ayyukansu a Nijeriya.

A lokacin da ya ke jawabi a madadin Shugaba Tinubu, Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima wanda kuma shi ne babban baƙo a taron ya bayyana amincewarsa ga cancantar sabbin jami’an, ya na mai kira a gare su da su kasance masu nagarta da ƙwarewa da kuma kare ƴancin Ɗan-adam a yayin gudanar da ayyukansu.

Ya ce, gwamnatin tarayya na cigaba da ƙoƙari wajen taimaka wa rundunar ƴan sanda da kuma tabbatar da walwala da jin-daɗin ma’aikatanta.

Ya ƙara da yin tsokaci game da gyare-gyare da su ke yi wajen ganin an inganta harkar tsaro a Nijeriya, inda ya ce sabbin jami’an za su taka rawar gani yayin cimma hakan.

By Babaji