Yadda ambaliya ta yi sanadiyyar mutuwar yara biyu da ɗaiɗaita sama da mutane 1,000 a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata ambaliya da akayi a Kafanchan da wasu ƙauyuka da ke kusa da garin a ƙaramar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna, ta yi sanadiyar rasa rayukan yara biyu tare da ɗaiɗaita mutane sama da 1,000.

Mataimakiyar kantoman Jema’a, Christy Usman ta bayyana hakan wa kwamitin kula da ɓarnar ambaliya a kudancin jihar a lokacin da ya kai ziyarar gani-da-ido a ranar Litinin.

Ta ruwaito cewa ambaliyar ta shafi cikin garin Kafanchan da gundumomin Jagindi, Atuku, Aso da Bade wacce ta kuma ɓarnata gonaki inda amfanin gona na miliyoyin kuɗi suka salwanta.

Ta ƙara da cewa, gwamnan jihar, Uba Sani ya yunƙura a lokacin da lamarin ya faru, ta na mai albishir da cewa nan ba da jimawa ba za a fara raba kayan jin-ƙai ga mutanen da lamarin ya shafa musamman waɗanda suka rasa gidaje da gonakinsu.

Sani Liman Kila, wanda shi ne shugaban kwamitin kuma shugaban ma’aikata, bayan duba matakin ɓarnar ambaliya a ƙananan hukumomin Sanga, Jema’a da Kachia ya bayyana cewa mutane da dama na buƙatar taimako na gaggawa.

Ya ce, cikin dalilan da suke sabbaba ambaliyar akwai tsukakkun gadaje, haramtattun magudanan ruwa da zubar da shara a wuraren da ba su dace ba.

By Babaji