Jiragen soji sun kashe ’yan ta’adda 28 a Neja

Spread the love

 Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan bindiga aƙalla 28 ne jiragen sojin saman Nijeriya suka hallaka a yankin Bassa, ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta ce jiragen sun ragargaji ’yan ta’addan ne da haɗin gwiwar sojojin ƙasa.

Mataimakin Darakta Yaɗa Labarai na Rundunar, Kyaftin Kabiru Ali, ya ce a yayin aikin sharar ’yan fashin daji ne sojojin suka yi arba da gungun wasu ’yan ta’adda kimanin 100.

Kyaftin Ali ya ce, “da samun rahoto ne jiragen suka je suka ragargaji ’yan ta’addan, inda aka gano gawarwakin 28 daga cikinsu.

“A halin yanzu ana ci gaba da kwaso makamansu da ababen hawansu, ana neman sauran ’yan ta’addan,” bayan harin na ranar Laraba, in ji sanarwar.

Jami’in ya bayar da tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba aikin tabbatar da tsaron jama’ar da murƙushe duk wata barazanar tsaro da ragowar ’yan ta’adda da ke hana jama’a sakat.

By ukarofi