Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Daga dukkan alamu babban titin Gwamnatin Tarayya, wanda ya haɗa biranen Gusau zuwa Funtua a jihohin Zamfara da Katsina ya zama tarkon mutuwa sakamakon yawaitar ayyukan ’yan ta’adda da ke tare hanyar kusan kullum.
Wakilin Blueprint Manhaja ya ruwaito cewa, babbar hanyar ta fuskanci hare-hare iri-iri sama da wata guda, inda ’yan ta’adda suka riƙa tare hanyar a kowacce safiya da kuma rana tsaka suna cin karensu babu babbaka.
Sai dai duk da kafa shingayen binciken sojoji da na ’yan sanda daga Funtuwa zuwa Gusau ɗin da Gwamnatin Tarayya ta yi, an yi garkuwa da matafiya da dama a kan hanyar cikin wata ɗaya da ya wuce zuwa yau.
A zantawarsa da Wakilin Blueprint Manhaja, wani matafiyi mai suna Malam Ibrahim Hussaini, ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohin da yankin ya shafa da su duba lamarin cikin gaggawa.
“Kamar yadda ku ke gani, ba mu da wata hanyar da za mu bi daga Funtuwa zuwa Gusau, domin ita ce hanya ɗaya tilo, kuma abin takaici ne a kullum waɗannan ’yan ta’addan da ake tsoro suna tare hanya suna garkuwa da matafiya har ma da kashe wasu daga cikinsu,” inji shi.
Malam Hussaini ya bayyana manyan shingayen binciken ababen hawa da aka samar a kan titin a matsayin marasa amfani, ya kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta sake yin masu garambawul tare da kawo wasu jami’an tsaron masu himma, domin kare lafiyar matafiya.
Ya ƙara da cewa, “Ba mu da ƙwarin gwiwa a kan jami’an tsaro da ke kan hanyar, kuma akwai buƙatar Gwamnatin Tarayya ta canza su kuma ta kawo waɗanda ke shirye, don kare matafiya da kuma yaƙar waɗannan ’yan ta’addan da suka addabi hanyar kusan kullum.”
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, wasu daga cikin wuraren da ’yan bindigar ke tarewa a kan hanyar Gusau zuwa Funtua sun haɗa da Magazu zuwa Tsafe, Magazu zuwa Kucheri, Kucheri zuwa ’Yankara da dai sauransu.
A jiya Alhamis ma rahotanni sun tabbatar da cewa, masu garkuƙa da mutanen sun yi awon gaba da wasu matafiya da ke kan hanyarsu ta Gusau, Babban Birninn Jihar daga Funtuwa da ke Jihar Katsina.
Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, kan lamarin ya ci tura har zuwa lokacin haɗa rahoton nan.
