Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar Hukumar Gwale, Hon. Garba Ibrahim ɗiso da cewa jajirtaccen wakili ne da yake kyakkyawan wakilci ga al’ummarsa.
Dakta Gaddafi Sani Shehu mataimakin Manajan Daraktan KHEDCO, sakataren yaƙin neman zaɓen Garba Diso ne a 2023 ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya ce a kowane lokaci ɗan majalisar na cuɗanya da al’ummar da jin buƙatunsu da tallafawa matsalolinsu da kawo aikace-aikace ta ɓangarori daban-daban duk da cewa aikin ɗan majalisa na yin doka ne amma yana ƙoƙarin yin ayyuka.
Ya ce suna alfahari da ɗan majalisar saboda irin jagoranci da yake a majalisar tarayya yana ƙoƙari sosai bayan taimakawa al’umma da yake na yau da kullum yana da tsare-tsare na ayyuka.
Ya ce abinda ya kamata mutane su gane shi ɗan majalisa aikinsa ya yi doka da za ta taimaki al’umma, amma saboda yanayi da ake suna saukowa ƙasa su bada gudunmawa cikin ayyuka da ya yi ya kawo fitilun kan titi guda 300 duk mazaɓu 10 na ƙaramar hukumar Gwale an sa 30.
Dakta Gaddafi Sani Shehu ya ce a ɓangaren cigaban ilimi a wannan shekarar ya samu dama kawo aikin gina rukunin ajijuwa guda 10 duk rukuni ɗaya yana da ajijuwa biyu, an ƙaddamar da ɗaya a mazaɓar ɗiso guda uku a ɗorayi, da Kadawa an ƙaddamar a kusada gidan Uba Safiyanu a Unguwar Fadama ɗorayi an ƙaddamar da gina rukunin ajijuwa ɗaya mai ajijuwa guda shida, waɗannan ayyuka za a ci gaba da su.
Ya ce waɗannan ayyuka da yake za su yi tasiri akan ci gaban ilimi wajen rage cunkoso a aji za a samu sarari da zai kawo kyakkyawan yanayi na koyo da koyarwa da inganta ilimi.
Sannan zai rage yawan yara da ba sa zuwa makaranta kuma wannan mataki ne da za a ci gaba da yi.
Dakta Gaddafi ya ce Garba Diso yana da kyakkyawan dangantaka da al’umma, baya ɓoye kansa daga garesu, ko bai sanka ba ka buga masa waya zai ɗauka ya saurareka, inji shi.
Dakta Gaddafi Sani Shehu ya ce a kowace mazaɓa yana da kwamiti idan ka tuntuɓesu da buƙata za a gabatar masa ya aiwatar da yardar Allah, sannan yana da kwamitin mata da suke wakiltarsa a mazaɓu.
Dakta Gaddafi ya yi kira ga mutanen Gwale su ƙara haƙuri kuma su riƙa gabatarwa ɗan majalisar buƙatun da zai taimaki cigaban al’umma a rubuce ga wakilansa ko bai yi nan take ba zai sa a tsari idan ya samu dama zai gudanar.
