Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya buƙaci Jam’iyyar PDP da ta janye matakin da ta ɗauka na ƙauracewa zaɓen ƙananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Satumba.
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC daga ƙananan hukumomi 8 na shiyyar Sanatan Sakkwato ta Gabas da suka yi dandazo a Goronyo domin gudanar da yaƙin neman zaɓen jam’iyya mai mulki.
Ya ce haryanzu shugabannin SIEC gwamnatin da ta shuɗe ta PDP ce ta naɗa su, kuma har yanzu sune suke ci gaba da shugabancin hukumar.
Ya bayyana mamakinsa na dalilin da ya sa PDP ke tsoron shiga zaɓen da SIEC za ta shirya.
Gwamna Aliyu ya tabbatar wa ‘yan PDP a jihar cewa SIEC a karkashin gwamnatinsa za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumoni na gaskiya da gaskiya.
“Na yi ganawa da shugaban SIEC kuma ya ba ni tabbacin gudanar da zaɓe na gaskiya, duk wanda ya yi nasara za a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.
Don haka gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su fito fili su zaɓi ‘yan takarar jam’iyyar don ci gaba da ayyukan da suka shafi jama’a a jihar.
