Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar tsaro na al’umma (Civil Defence), sun samu nasarar kama tsoho ɗan shekara 60 da satar wayar wutar lantarki a ƙaramar hukumar Funtuwa.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar DSC Buhari Hamisu ya bayyana sunan ɓarawon mai sun Hassan Abubakar da ke zaune a ƙauyen Lasanawa a garin Maska da ke ƙaramar hukumar Funtuwa.
DSC Buhari ya bayyana cewa Hassan ya zo hannun jami’in tsaro ne bayan an ganshi da tsinkakkun wayar wutar lantarki yana ƙoƙarin kaiwa masu cinikin kayan nauyi a garin Funtuwa.
“Cikin dare ya hau sandar wayar wutan lantarkin da ke kan babban titin Lasanawa inda ya tsinci wayar ya sanya a buhu da ƙoƙarin kai wa masu cinikin kayan nauyi a garin Funtuwa kan jami’an su su rutsa da shi mai laifin,” DSC Buhari ya ce.
Jami’in yaɗa labaran ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma yanzu haka yana tsare a hedkwatar su da zarar sun gama bincike za su gabatar da shi a kotu.
Kwamandan hukumar tsaron na jihar Jamilu Indabawa ya yaba wa jami’ansa a bisa namijin ƙoƙarin da suke wajen daƙile aikace-aikacen ɓatagari a faɗin jihar.
Haka kuma Indabawa ya yaba wa al’ummar jihar wajen goyon bayan da suke ba hukumar wajen yaƙar batagari musamman masu sace wayar wutar lantarki a manyan titunan jihar.
