Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Alƙaliyar Alƙalan jihar Adamawa, mai shari’a Hasfat Abdulrahman, ta bayar da umarnin a saki wata mata mai suna Saraya Silma ‘yar shekara 60 da ta shafe shekaru 10 tana jiran shari’a a gidan gyaran hali na Yolde-Pate da ke Yola, babban birnin jihar.
BBC Hausa ta rawaito cewa an zargi Silma da maita wanda daga baya mai ƙorafin ya gano ba shi da tushe balle makama.
Wannan sakin dai na cikin wani ɓangare na aikin wani kwamiti na gidajen yari a jihar Adamawa, karkashin jagorancin babbar jojin, inda aka sallami fursunoni 32, da bayar da belin wasu 25, da kuma yankewa 37 hukunci daga cikin mutum 182 da ke jiran shari’a.
Wasu daga cikin waɗanda aka sallama an ba su ayyukan yi wa al’umma hidima, kamar tsaftace wuraren jama’a a yankunansu.
Kurkukun Yolde-Pate,wanda ƙarfinta ɗaukar fursunoni 800 ne kawai na ɗauke da fursunoni 886 a halin yanzu.
Daga cikin waɗannan fursunoni, mutum 665 suna jiran shari’a, 185 kuma an yanke musu hukunci, 10 na zaman ɗaurin rai-da-rai, yayin da kuma16 ke fuskantar hukuncin kisa
