Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Spread the love

Kungiyar Fenerbahce ta amince ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan Serbia mai shekara 31, Filip Kostic daga ƙungiyar Juventus ta Italiya.

Memphis Depay, da yanzu haka bashi babu kuɗi a kansa bayan baro Atletico Madrid, ya kammala duba lafiyar domin cimma sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar Corinthians ta Brazil.

Kyeftin ɗin Liverpool virgil van Dijk mai shekara 33, da kwantiraginsa ke daf da karewa, ya ce yana son tsawaita kwantiraginsa ta hanyar cimma sabuwar yarjejeniyar da za ta bashi dama cigaba da kasancewa da ƙungiyar har zuwa shekara ta 2026.

Arsenal ba ta da niyyar bai wa ɗan wasan tsakiya na Italiya Jorginho damar barin ƙungiyar, duk da cewa Galatasaray ta nuna tana son saye ɗan wasan mai shekara 32 kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa a Turkiyya.

Barcelona na harin ’yan wasa biyu, Jonathan Tah mai shekara 28 daga Bayer Leɓerkusen da Joshua Kimmich mai shekara 29 daga Bayern Munich, dukkaninsu daga Jamus, yayin da take cikin rashin tabbas kan makomar ‘yan wasanta biyu, Ronlado Araujo mai shekara 25 daga Uruguay da kuma Frenkie de Jong mai shekara 27 daga Netherlands.

Paris St-Germain na ƙoƙarin ganin ta tsawaita kwantiraginsa kocinta, Luis Enriƙue, da ke karewa a watan Yunin 2025.

ɗan wasan gaba a Canada, Jonathan Daɓid, da ake alaƙantawa da Chelsea a wannan kaka, ya ce ya tattauna da ƙungiyoyi daban-daban amma ya zaɓi cigaba da zama a Lille. Matashin mai shekara 24 ya nuna cewa yanzu haka yana tattauna batun tsawaita zamansa da ƙungiyar ta Faransa.

Atletico Madrid da Barcelona da Juɓentus na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan Arsenal da Ghana mai shekara 31, Thomas Partey.

Manchester United da Newcastle United na zawarcin ɗan wasan Faransa mai shekara 29, Adrien Rabiot, da yanzu haka kwantiraginsa ke daf da karewa a Juɓentus.

Manchester City, da Chelsea da kuma Liɓerpool na sha’awar matashin ɗan wasan tsakiya na Sunderland Chris Rigg na Ingila mai shekara 17.

ɗan wasan tsakiya na Ingila da Lille Angel Gomes shi ne babban wanda Newcastle take son saye amma kuma Liɓerpool, da Tottenham da Borussia Dortmund su ma suna son ɗan wasan mai shekara 24.

West Ham na shirin karɓar tayi daga Galatasaray a kan ɗan bayanta na Italiya Emerson Palmieri.

ɗan bayan Faransa Wesley Fofana, mai shekara 23, ya ce yana tunanin barin Chelsea domin ya koma ƙungiyar garinsu Marseille a bazaran nan.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta tattauna da wasu masu horarwa da dama duk da ƙoƙarin da Lee Carsley ke yi a matsayin kociyan riƙon ƙwarya na Ingila.

Tsohon kocin Ingila Gareth Southgate, mai shekara 54, ya ce watakila aikinsa na gaba ya kasamnce ba na ƙwallon ƙafa ba ne.

Mauricio Pochettino, zai riƙa karɓar albashin da ya kai dala miliyan 6 a duk shekara a matsayin kocin Amurka.

FIFA na tattaunawa domin ƙara yawan ƙasashe a gasar kofin duniya ta mata zuwa 48 a shekara ta 2031, kamar yadda ake yi a gasar maza.

Har yanzu Chelsea da Tottenham na son matashin ɗan bayan Lecce, Patrick Dorgu mai shekara 19 ɗan Denmark wanda aka yi masa kuɗi kusan yuro miliyan 40.

Tottenham, da Newcastle da Arsenal na kan gaba a masu neman sayen ɗan gaban Lille, Jonathan Daɓid, ɗan Kanada to amma Juɓentus ma na so.

Chelsea na son ɗan bayan Monaco da Brazil ɓanderson, mai shekara 23, to amma Manchester United da Tottenham ma na cikin masu sonshi.

By ukarofi