APC ga Kwankwaso: Ba a bar rabon tallafin abinci a hannun gwamnatin NNPP ba saboda gudun handama

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar adawa ta APC a jihar Kano, ta soki Dakta Rabi’u Kwankwaso, jagoran jam’iyyar NNPP, bisa sukar da ya yi wa tsarin rabon tallafin kayan abinci da gwamnatin tarayya ta yi.

A cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na jiha , Abdullahi Abbas ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar rage yunwa a ƙasar nan, amma gwamnatin NNPP a Kano na kawo cikas ga wannan ƙudirin.

Ya ce Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da wasu matakai na tallafawa marasa galihu da marasa ƙarfi amma waɗanda aka ba su don raba wa al’umma a Kano na karkatar da kayan.

Abbas ya ba da misalai da yadda ake zargin wasu manyan jami’an gwamnatin NNPP da hannu wajen karkatar da kayan abincin.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya yi kira ga Kwankwaso da ya umurci gwamnansa da ya binciki waɗannan abubuwan da suka faru tare da tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika sun girbi abinda suka shuka a kotu.

Ya kuma soki Kwankwaso da cewa ba a hannun APC kaɗai aka bar aikin rabon ba.

A cewar Abbas, kwamitin da gwamnatin tarayya ta sake kafa wa ya haɗa da mambobin jam’iyyun siyasa daban-daban da suka haɗa da NNPP da PDP da kuma IPAC.

By ukarofi