Kano Pillars ta yi nasarar doke Ikorodu United 3-0 ranar Lahadi a wasan makon farko da fara gasar firimiyar Nijeriya ta 2024/25.
Pillars ta buga wasan ne a jihar Katsina, bayan da ake gyaran filin wasanta na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, Nijeriya.
Pillars ta ci ƙwallayen ta hannun Mustapha Umar da Rabiu Ali da ya zura biyu a raga, mai shekara 43 yana buga kaka ta 18 a babbar gasar tamaula ta Nijeriya.
Da wannan sakamakon Pillars, wadda ake kira sai masu gida tana ta ɗaya a kan teburi da maki uku, sai Sunshine Stars ta biyu da maki uku.
Enyimba ce ta uku da maki uku, sauran da suke da maki uku a karawar makon farkon sun haɗa da Remo Stars da Niger Tornadoes da Plateau United.
Wannan kakar ce ake kokarin ɗora jadawalin wasannin firimiya na Nijeriya, domin a kammala gasar lokaci ɗaya da na sauran ƙasashen duniya.
Hakan zai bai wa ƙungiyoyin damar shirin shiga gasar zakarun Turai da sauran manyan wasanni a kan kari da samun hutun ’yan ƙwallo iri ɗaya da na sauran gasar duniya
