Baki-biyu: Alƙalin da ya umarci Yahaya Bello ya kai kansa kotu, ya haramta wa EFCC kama tsohon jami’in Ekiti

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya aika wa hukumar EFCC takardar dakatar da ita kama tsohon Daraktan mallakar kadarori, O’Seun Odewale na Ekiti wanda ake zarginsa da sauya akalar wasu kuɗaɗe na aikin filin jiragen sama na jihar.

Har’ilayau kuma, Nwite shi ne alƙalin da ya umarci tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da ya gabatar da kansa a gaban kotu kan zargin almundahana na N80.2b sakamakon ƙarar sa da EFCC ta kai.

A ranar 22 ga watan Oktoban 2022 ne jaridar ‘ShaharaReporters’ ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar, Kayode Fayemi ya ƙaddamar da aikin kammala filin jiragen sama na Ado-Ekiti, babban birnin jihar wanda ake sa ran zai taimaka wajen haɓaka tattalin arziƙin Ekiti da al’ummarta.

Jaridar da ruwaito cewa, akwai ayyuka da dama da ba a kammala ba a filin jirgin har zuwa yanzu.

Daga baya, gwamnatin jihar ta gano cewa ba a yi aikin filin jirgin ba duk da cewa tsohuwar gwamnati ta bada aikin.

Don gudun tuhuma, Odewale da wani Ariyo Oyinkolawa Adesola suka shigar da takardar, zuwa ga Alƙali Nwite, saboda ya hana EFCC kai wa tsohon jami’in samame kan al’amarin.

A sakamakon haka ne la’akari da wasu dalilai, Alƙali Nwite a yayin hukunci ya nemi ɓangarorin biyu su saurara har zuwa ranar 26 ga watan Satumba, 2024 wanda a lokacin ne za a cigaba da zama kan batun.

By Babaji