Tsohon gwamnan Kogi ya amsa gayyatar EFCC

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya amsa gayyatar da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta yi masa bayan shafe watanni ana kai-kawo da kuma yunƙurin da hukumar ta yi na kama shi.

Wata sanarwa da daraktan ofishin yaɗa labarai na Yahaya Bello, Ohiare Michael, ya fitar a ranar Laraba, ta ce Bello ya mutunta gayyatar da EFCC ta yi masa “bayan tuntuɓar iyalansa, da lauyoyi da kuma abokan siyasa.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “tsohon gwamnan, wanda ke matuƙar mutunta doka da oda, ya nemi a bi masa haƙƙinsa ne kawai domin a tabbatar da bin doka da oda.

“Tsohon Gwamnan ya yi amanna da ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ɗora Nijeriya kan turbar ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa, kuma yana goyon bayan yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.

Muna fatan hukumar za ta kasance mai ƙwarewa kamar yadda ya kamata tare da mutunta muhimman haƙƙoƙinsa a matsayinsa na ɗan ƙasa a tarayyar Nijeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, “Za a bayyana cikakken bayanin hulɗarsa da jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.”

Matakin na zuwa ne bayan mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya ɗage ci gaba da shari’ar kan zargin almundahanar kuɗaɗe da EFCC ta shigar a kan Bello zuwa ranar 25 ga watan Satumba.

Idan dai ba a manta ba EFCC ta gurfanar da Bello ne a gaban kotu kan tuhume-tuhume 19 da ake zargin sa da karkatar da kuɗaɗen da suka kai Naira biliyan 80.

By ukarofi