Daga RABI’U SANUSI
Gwamnatin Jihar Kano tace ta Ƙuduri aniyar gina gidajen da za ta tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a faɗin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a yayin gudanar da zaman majalisar zartawa karo na 19.
Gwamnan yace tuni shiri yayi nisa wajen gabatar da wannan shiri ta ofishin ma’aikatar kula da harkokin jin ƙai da ofisoshin da ke tallafawa waɗanda ibtila’i ta sama.
Abba Kabir yace kamar yadda ya samu bayanai da dama tare da zuwa da kansa da ganin waɗansy guraren dan tabbatarwa tare da jajantawa.
”Kamar yadda kuka sani wannan gwamnati na tsaye kan ƙafafun ta dan ganin tayi dukkan mai yuwuwa dan ƙara kawo cigaba a wannan jiha tamu mai albarka.
Hakan nan kuma gwamna ya bayyana jajantawa ga gwamnatin Jihar Borno bi sa ambaliyar ruwa da ya shafi kafatanin jihar.
Haka zalika gwamnan yace yayi matuƙar nuna farin ciki bisa yadda yaga ɗalibai su ka koma makaranta a jiya Talata tare da sama ma ɗaliban gurin zama.
”Ya zuwa yanzu kusan shirin mu yayi nisa matuƙa wajen samar ma da ɗaliban mu kujeru sama da 70,000.
Gwamnan ya kuma ƙara taya al’ummar musulmi murna bisa zagayowar watan fiyayen halitta Annabi S.A.W.
Sannan ya ƙara tabbatar ma da al’ummar Jihar Kano cewa gwamnatin sa za ta cigaba da kawo ayyukan cigaba.
