Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Matasa guda 300 da suka fito daga ƙananan hukumomi 11 na shiryar Funtuwa a jihar Katsina suka samu horo na kwana guda akan yadda za su yi kiwon kifi.
Sanata Muntari Dandutse mai wakiltar shiyar Funtuwa ne ya ɗaki nauyin horaswar tare da basu kowanne Naira dubu ɗari bayan kammala samun horon .
Mataimaki na musamman ga ɗan majalisar dattijan Abdullahi Nuhu Kurfi ya bayyana wa manema labarai haka a garin Funtuwa
Ya ce a baya ma Sanata ya ɗauki nauyin horas da matasa 400 koyon yin takalma da suma kowannen su Sanata ya ba Naira dubu tamanin domin su tsaya da ƙafafunsu.
Abdullahi Kurfi ya nuna cewa waɗannan shiri da Sanata ya aiwatar na daga cikin ƙudirin ɗan majalisar na samarwar matasa aikin yi da kauda su daga shiga miyagun halaye.
Haka kuma sabuwar Jami’ar Kimiyya da Fasaha da gwamnatin tarayya ta kafa a Funtuwa nan bada jimawa ba za su fara zangon karatu Abdullahi Kurfi ya ce.
Ya ƙara da cewa Sanata ɗandutse ne ya kawo ƙudirin ƙirƙiro da jami’ar a yankin da yanzu haka hukumar kula da jami’o’i na ƙasa za su ziyarci jami’ar domin ganewa idanunsa akan shirye-shiryen fara zangon karatu a jami’ar.
Shi ma a bayaninsa shugaban kwamitin kula da ayyuka na ɗan majalisar Abdullahi Sabuwar ƙasa ya faɗi wasu aikace-aikace da Sanata ya aiwatar a yankin da ya haɗa da gina ɗakin karatu a garin Malumfashi.
Saura kuma akwai gina ofishin ‘yan sanda a garin ƙanƙara da gina madatsan ruwa a garin Bakori.
Sanata Muntari ɗandutse ya kuma shimfiɗa kwalta a hanyoyi da dama a shiyyar.
