Ya kamata gwamnati ta tallafa wa mutanen da ambaliya ta shafa a Maiduguri – Ado Garba Bichi

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Wani babban mahauci a Legas mai gudanar da harkokin sana’arsa Tafawa a babbar mayankar shanu ta abbatuwa Okoba Agege dake cikin garin Legas mai suna Alhaji Ado Garba Araba ɗan asalin ƙaramar Hukumar Bichi a cikin jihar Kano, ya shawarci Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da gwamnatin jihar Borno da Jigawa da sauran gwamnatocin jihohin ƙasar nan da su tausayawa mutanen da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Borno da sauran makamantansu inda a cewarsa a sanadiyyar hakan waɗansu daga cikin al’ummar jihar Borno da Jigawa suka tafka mummurnar asarar rayukan ‘yan uwa tare da dukiyoyinsu gaba ɗaya.

Alhaji Ado Garba ya yi wannan tsokaci ne a Legas a lokacin da yake nuna rashin jin daɗinsa dangane da faruwar wannan al’amari.

Ya jajenta wa waɗanda lamarin ya shafa, da fatan Allah Ubangiji ya jiƙan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya sanadiyyar faruwar wannan al’amari.

Haka zalika Ado Garba ya ci gaba da cewa su kuma waɗanda suka tafka asarar gidaje da dukiyoyinsu ubangiji  Allah ya mayar masu da mafificin abinda suka rasa baki ɗaya. Haka kuma ya ce yana mai gabatar da saƙon ta’aziyarsa ga mai martaba Sarkin Borno Alhaji Garbai Shehu da gwamnonin jihar Borno da Jigawa a ƙarƙashin jagorancin gwamnonin jihohin guda biyu Alhaji Dakta Babagana Umara Zulum da Gwamnan jihar Jigawa Dakta Alhaji Umar Mamadi ɗan Modi da sauran gwamnatocin jihohin da suka gamu da irin wannan iftila’i na ambaliyar ruwa a Nijeriya baki ɗaya.

Sannan ya ci gaba da shawartar ‘yan uwansa mahautan jihar Legas dama na ƙasa baki ɗaya da su cigaba da gudanar da sana’ar su ta fawa a cikin tsafta tare da tausayawa kostomomi masu sayan nama a kowanne lokaci.

Haka kuma ya cigaba da jawo hankulan’ ‘yan Nijeriya a cewarsa musamman ‘yan masu ra’ayin zagin shuwagabanni da su kaucewa yin hakan a matsayinsu na ‘yan ƙasa nagari, maimakon hakan zai fi dacewa su cigaba da yi wa shuwagabannin addu’a domin neman amincewar Allah ubangiji a wajen karkato da  zukatan shuwagabannin yadda za su cigaba da jagorancin al’umma a cikin adalci.

ƙarshe ya cigaba da jawo hankulan ‘yan Nijeriyar da su cigaba da zaman lafiya da junansu domin ciyar da ƙasar gaba.

By ukarofi