An ja kunnen kafafen yaɗa labarai mallakin jihar Kebbi kan ƙara ƙaimi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Mai bai wa Gwamnan Kebbi shawara kan dabarun aikin jarida Malam Abdullahi Idris Zuru ya ja kunnen kafafen yaɗa labarai musamman mallakar jihar kan su ƙara ƙaimi wajen yaɗa ayyuka da manufofin gwamnatin Malam Nasir Idris ƙauran Gwandu.

Ya yi wannan kiran ne ranar Litinin ɗin da ta gabata yayin wani rangadi da ya ke a kafafen yaɗa labarai da ke jihar da suka haɗa gidan Talabijin da Rediyo (KBTɓ da KBC) mallakar jihar da gidajen Rediyon ɓision da Nagari FM mallakar ‘yan kasuwa da kuma gidan rediyon Eƙuity FM da kuma NTA mallakar gwamnatin tarayya.

Ya ƙara da cewa babu dalilin yin ƙasa a gwiwa wajen gudanar da ayyukan yaɗa manufofin ƙauran Gwandu saboda ya inganta kafafen yaɗa labarai mallakar jihar da kuma ma’aikatar yaɗa labarai ita kanta saɓanin inda aka fito a baya da aka yi watsi da su aka yi musu riƙon sakainar kashi.

Malam Abdullahi Idris Zuru ya bayyana cewa gwamna Nasir Idris yana da sha’awa da ayyukan yaɗa labarai saboda haka ne ma ya ɗauki matakan ingantasu ta hanyar zamanantar da su “saboda haka ya kamata su ma ma’aikatan su ƙara ƙaimi wajen yada manufofi da ayukan wannan gwamnati.”

Ya kuma nemi haɗin kan kafafen yaɗa labarai mallakar ‘yan kasuwa da ke zaune a Kebbi da su ma su bayar da na su gudummawa wajen yaɗa manufofin ƙauran Gwandu musamman wajen wanzar da zaman lafiya da ayyukan cigaba da ya ke aiwatarwa.

Babban manajan gidan Talabijin na KBTV mallakar jihar Malam Aminu Sani Kamba ya bayar da tabbacin wannan ƙoƙarin na maigirma gwamna Nasir ba zai tafi a banza ba saboda ya sha alwashin yin duk abin da ya kamata don ganin an yayata ayyuka da manufofin cigaba da gwamantin ke yi.

Haka-zalika takwakwarorinsa na sauran kafafen sun bayar da tabbacin nasu goyon baya inda Malam Umar Balarabe na Eƙuity FM ya nemi gwamnatin Kebbi da ta tallafawa wannan gidan rediyon da waɗansu kayan aiki musamman abubuwan hawa tare da ɗaukar nauyin waɗansu shirye-shirye ta yadda za su samu ƙarin kuɗin shiga.

By ukarofi