Bai dace NNPCL ya ƙayyade farashin man fetur ɗin Dangote ba – Falana

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban lauya a Nijeriya kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil adama, Femi Falana, ya ce, karya doka ne yadda kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya ƙayyade farashin man fetur ɗin matatar Dangote, bayan ya fara jigilarsa.

Wata sanarwa da Falana ya fitar a ranar Talata ta ce matakin da NNPCL ya ɗauka ya saɓa wa sashe na 205 na dokar masana’antar mai (PIA).

Ya ce, “A ranar 5 ga Satumba, 2024, Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NNPCL) ta bayyana cewa rashin daidaiton kudaden waje ya kasance wani muhimmin al’amari da ya haifar da tashin gwauron zabi na man fetur.

“Hukumar NNPCPL tana bayanin farashin fetur ɗin da aka shigo da su cikin ƙasar a lokacin. Musamman, Mataimakin Shugaban Kamfanin Mai, ɓangaren wadatar man fetur na NNPC, Adedapo Segun, ya bayyana cewa sashe na 205 na hukumar PIA da ta kafa kamfanin NNPC, ya bayyana cewa ‘yan kasuwa ne ke tantance farashin man fetur.

A cewarsa, “An daidaita kasuwar, ma’ana cewa yanzu haka farashin man fetur na hannun jami’an kasuwa ne maimakon gwamnati ko kuma kamfanin NNPC.

Bugu da ƙari, farashin na taka rawar gani wajen yin tasiri a kasuwa.

“Amma sabanin wannan sanarwa da aka yi ta yaɗawa, NNPCL ta ƙayyade farashin man fetur da kamfanin matatar man Dangote ya samar. Matakin da hukumar ta NNPC ta ɗauka, ya saɓa wa sashe na 205 na PIA, wanda ya tanadi cewa ‘yan kasuwa ne za su tantance farashin man fetur.

By ukarofi