Cinikin da muke a rana yanzu da ƙyar yake samuwa a sati – Tijjani Bashir

Spread the love

Daga BUSHIRA NAKURA

TIJJANI ISAH BASHIR jajirtaccen matashin ɗan kasuwa ne mai neman na kansa a birnin Kano. A zantawarsa da Wakiliyar Blueprint Manhaja, Bushira Nakura, ya bayyana mana yadda al’amuran ciniki da kasuwanci suka sauya yanzu bayan rikicewar harkokin tattalin arzikin al’ummar Nijeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Assalamu alaikum warahamatullah wabarakatuhu. Mai karatu zai ji daɗi idan ka faɗa mana cikakken sunanka da sunan da aka fi saninka da shi, sannan da tarihinka a taƙaice.

TIJJANI: Amin waalaikumussalam warahamatullah wabarakatuhu. Sunana Tijjani Isah Bashir. Ana kira na da Tijjani. Na taso a Unguwar Garke Kwanar Dala. Na yi makarantar allo a Dala wajen Malam Sadauki da zuri’arsa, na yi makarantar islamiyya ta dare a nan Garke wadda a ke kira Ihiyaudeenil Islam, Kwanar Dala. Na yi karatun littattafai da dama Alhamdulillah. Na yi primary a makarantar Dambazau Islamiyya primary school, na yi secondary junior a makarantar Audu Danbatta ƙofar Ruwa, na yi senior secondary a makarantar shahuchi wadda a ka fi sani da Aliya, sannan na yi NCE a makarantar Federal College of Education Kano, wadda aka fi sani da FCE kano.

Ka na sana’a ne ko aikin gwamnati?

Ni ɗan kasuwa ne a kasuwar sabon gari da ke kano.

Ka na da aure in kana da ‘ya’yanka nawa?

Ina da aure Allah ya albarkace ni da ‘ya’ya bakwai, amma ɗaya ya rasu, yanzu shida ne a raye.

Meye sana’arka?

Sana’ata sayar da ‘underwears’ na maza.

Me ka karanta?

Na karanci Hau/Pes, ma’ana Hausa/Primary Education.

Idan ka samu dama za ka iya ci gaba da karatu?

Eh ina da burin ci gaba da karatu in na samu damar hakan.

Ba ka sha’awar aikin gwamnati ne ya sa ka zaɓi layin kasuwanci?

Ina sha’awar aiki amma samun aikin ne wahala a yanɗu, shiyasa na ke taɓa kasuwanci.

Yaya mu’amala da zaman takewa take gudana a kasuwar Sabon Gari?

Zamantakewar kasuwar Sabon Gari kamar ko wanne kasuwa mu na zaune cikin lumana ana zaman lafiya da abokan kasuwanci sai ɗan abinda ba a rasa ba na ƙalubale, amma yanzu yanayin kasuwa ba ciniki abinda za ka iya cinikin sa a rana ɗaya yanzu idan ka samu a sati ma sai sam barka.

Rayuwa ta yi tsada sosai fiye da tunanin mutane. Ko ya take agunka?

To, ba abinda zan ce sai godiyar Allah, amma a wannan zamanin duk mai ƙaramin ƙarfi ai yana rayuwa ne cikin yanayi na takura da tsadar rayuwa,

Wallahi idan ina kallon yanayin da na san wasu a baya da yanzu sai na ji tausayin kanmu bakiɗaya, domin mafi akasarin mutane sun fita hayyacinsu, ba a iya samun cin abinci koda sau biyu a rana, ka ji wani ya kwana ya wuni bai ci ba ga iyali abin na ɗaga min hankali, 

A yanzu da kyar mutane ke iya samun abinda za su ci a rana sau ɗaya. A ganin ka laifin waye mutane ko Gwamnati?

Gaskiya ni na fi ganin laifin gwamnati domin duk abinda ke faruwa ita ce sila ta tsaurara ta takura ta uzzura, wasu ‘yan kasuwarmu kuma sun ƙara assasa tsadar.

Yanzu a ce za ka samu zama da shugaban ƙasa ko ‘yan majalisarmu na tarayya wacce shawara za ka iya ba su?

Shawarar da zan ba su ita ce, su tausayawa talaka, su na amfani da kuɗaɗɗenmu su na gina kansu da iyalansu amma talaka na cikin damuwa, maganar gaskiya a yi duk mai yiyuwa a shigo da kayan abinci daga ƙasashe kamar yadda a ke a baya hakan zai sauƙaƙa kayan, sannan a hana fita da namu kamar yadda ake a yanzu. 

Meye kake ganin idan akace yau anyi shi mutane zasu samu sauƙin rayuwa?

Gaskiya a buɗe border abinci zai sauƙi da ikon Allah, gwamnati ta taimaka wa asalin manoma da kayan noma, a shigo da takin zamani wanda gwamnati ta hana shigo da shi a yanzu. Ina ga hakan zai sauƙaƙawa talaka.

Yaya kake kallon rayuwar da da ta yanzu?

Ina ai rayuwar yanɗu gabaɗaya ba ma za a haɗa ta da ta baya ba wajen sauƙi, a baya ko ba ka da kuɗi za ka samu abinci ka ci, a yanzu kuwa wanda yake ƙoƙarin bayarwa ma nema ya ke shi ma saboda tsadar rayuwa, dan haka a da muna rayuwa cikin kwanciyar hankali ba yunwa, a yanzu kuwa yunwa kaɗai na kashe al’umma wallahi.

Ko ka na da wani buri da kake son cikawa?

Burina Allah ya canja mana wannan shuwagabanni da masu adalci wanda talakawa za su samu sauƙin rayuwa walwala da kwanciyar hankali su dawo a ƙasarmu a daina wannan kashe kashe da ake da sunan addini ko yare.

Sannan ina da burin Allah ya min suttura na taimaka wa marasa shi da ƙarfin ikonsa, domin ina son na ga ina taimaka wa ina jin daɗin hakan.

Wacce shawara za ka bai wa mutane da shugabanni?

Shawara ga shugabanni su ji tsoron Allah, su cire son rai su saka buƙatar talakwa a gaban tasu. Shawara ga talakawa mu duƙufa da addu’a sannan mu daina biyewa son zuciya muna zaɓar wanda mu ka san kuɗi suke ba mu mu zaɓa, mu koma zaɓar cancanta.

Wane abu ne na farin ciki wanda ba za ka taɓa mantawa da shi ba?

Abin farin cikin da bazan taɓa mantawa ba shi ne ranar aurena ba zan manta da wannan ranar ba, kuma ya saka ni farin ciki matuƙa.

Wane abu ne na baƙin ciki wanda ba za ka taɓa mantawa da shi ba?

Rasuwar ɗana Amir, ba zan taɓa mantawa da ita ba, saboda shaƙuwata da yaron yana ƙaunata, domin ita ce mutuwa da na sani tunda mahaifana na nan a raye.

Meye yake baka tsoro a rayuwa?

Wannan yanayin da ƙasar ke ciki yana ban tsoro, kowa ya samu dama burinsa ya yi zalunchi, ga kashe kashe kullum kana fargaba ko zaka dawo ko ba za ka dawo ba.

ƙasashe nawa ka taɓa zuwa?

Nijar kawai na taɓa zuwa a ƙasashen duniya.

Jahohi nawa ka taɓa ziyar ta?

Naje aƙalla sama da 20 a Nijeriya.

Ko akwai ƙasar da ka ke son zuwa idan hali ya samu?

E, ina na burin Allah ya kai ni Saudiya na sauke farali na roƙi Allah na ziyarci kabarin Annabi sallallahu alaihi wasallam.

Me ka fi so a yi ma ka kyauta da shi?

Ina son kyautar turare saboda ina sonsa sosai.

Wane abu ne ya ke saurin saka jin haushi?

Zalunci da ƙazafi suna saurin saka ni fushi, ba na son a min ƙazafi ko na ga ƙiriƙiri ana zaluntata ba yadda zan yi, wannan abu na damu na.

Wane kalar abinci da abin sha ka fi so?

Na fi son wake da shinkafa a abinci bana gajiya da shi. Abin sha na fi son ‘ya’yan itace. 

Yanayin gari wanne ka fi so damina sanyi da zafi?

Na fi son sanyi.

Meye ka ke so ga mutane?

Idan Allah ya ba ka iko ka taimaki mutane da ina son masu taimakon al’umma.

Ko akwai abinda ka ke son cewa wanda ya shafe ka ko al’umma wanda ba a tambaye ka ba?

Abinda na ke so mutane su guji yaɗa jita-jita domin yana daga cikin abinda ke ƙara lalata mana rayuwa, sannan mu taimaki juna dan Allah. Abinda na ke son cewa da ya shafi al’umma bakiɗaya shi ne mu san ciwon kanmu, mu koma ga Allah, mu taimka wa juna dan Allah, Allah zai taimaka mana ta inda ba mu zata ba.

Su waye gwanayenka a duniya?

Gwanaye na su ne babana da mamana, sai malamaina.

Wacce nasiha za ka yi wa matasa musamman ci ma zaune wanda ba su son nema?

Matasa su tashi su nemi na kansu, wannan rayuwar in baka da shi da kai da babu duk ɗaya a wajen mafi akasarin mutane.

Ko ka na da wanda za ka gaisar?

Ina son na gaisar da Malam Abdullahi Uwais Madabi, Malam Aminu Daurawa, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Engr Abba Kabir Yusuf.

Fatan ka ga jaridar Blueprint Manhaja?

Eh, Ina ganinta kuma Ina yabawa da aikinsu Allah ya yi musu jagora da mu bakiɗaya.

Mun gode.

Ni ma na gode.

By ukarofi