Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya bayyana kyakkyawan yaƙinin cewa ta’addancin da Bello Turji ke yi a faɗin Jihar Zamfara ya zo ƙarshe, yayin da ya ce a yanzu Turji ya gudu zuwa kan iyakar Zamfara da Sokoto, wajen yankin Shinkafi.
Lawal ya bayyana haka a ranar Litinin, cikin wata tattaunawar da gidan talbijin na Channels tare da Seun Okinbswole.
Gwamna Lawal ya bayyana hakan kwana uku bayan sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe gogarma Halilu Sububu, a Jihar Zamfara.
Lawal ya ce wannan ƙoƙarin da sojoji suka yi, zai iya daƙile ayyukan ta’addanci sosai a yankin Zamfara da Sokoto.
Da aka tambaye shi batun irin su gogarma Bello Turji, sai Lawal ya ce “A irin wannan ƙoƙari da kuma haɗin kai da kuma mu gwamnatin jihohi, Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomin tsaro, to nan ba da daɗewa ba za a kashe Bello Turji.”
Sai dai ya ce ko da sojoji ba su kakkaɓe ‘yan bindiga baki ɗaya ba, to kisan Sububu da kuma samun nasarar kashe Turji da ake ƙoƙarin yi, wata babbar nasara ce da za ta rage ta’addanci sosai da sosai a yankin.
Dangane da tsamin dangantaka tsakanin sa da Bello Matawalle, tsohon Gwamnan Zamfara wanda Gwamna Lawal ya kayar a zaɓen 2023, ya ce tankiyar da ke tsakanin sa da a samo asali ne daga yadda Matawalle, wanda a yanzu shi ne ƙaramin Ministan Tsaro, ya riƙe akalar Jihar Zamfara a lokacin da ya ke Gwamna.
Lawal ya ce kafin ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, ya taras Hukumar EFCC na binciken salwantar Naira biliyan 70 a hannun Matawalle.
Ya ci gaba da cewa a lokacin da shi kuma ya hau mulki, gwamnatin sa ta yi bincike, ta rasa abin da gwamnatin Matawalle ta yi da Naira biliyan 250.
Daga nan Lawal ya ƙara lissafa kuɗaɗen da ake zargin Matawalle ya wawura daki-daki.
Lawal ya a ce ko Naira miliyan 4 Matawalle bai bari a asusun Gwamnatin Zamfara ba.
Ya ce Matawalle ya sauka ya bar bashin masu kuɗin fansho Naira biliyan 13 an kasa biyan su.
Ya ce Matawalle ya sauka ya bar bashin kuɗaɗen jarabawar ɗalibai Naira biliyan 1.6, kuma ya bar bashin kudin wuta har Naira biliyan 1.3.
