Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata sanarwar da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Tsaron Jiha ta Jihar Barno ta fitar a ranar Talata, a shafin ta na Facebook, ta yi kakkausan gargaɗin cewa jama’a su guji sayen kayan miyar da gawarwakin jama’a da dabbobi da kuma dagwalon ruwan najasa suka sa wa cututtuka sanadiyyar garwaya da ambaliya.
Sanarwar ta ƙara da cewa haka kuma sinadarai masu guba duk sun gauraya da kayan miyar, irin su alayyahu da sauran kayan lambu da ake amfani da su wajen miya.
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Tsaron Jiha ta ce, “sanadiyyar ibtila’in ambaliya, kayan miya masu yawan gaske sun gurɓace da cututtuka daga gawarwaki, mushen dabbobi har ma da dagwalon ruwan najasa da sinadarai masu guba da ƙwayoyin cuta na daban-daban.”
Kan haka ne gwamnati ta yi gargaɗin cewa cin waɗannan kayan miya ko kayan marmari babbar barazana’ ce ga lafiyar jama’a, kuma za a iya ɗaukar cututtukan da ake kamuwa da su daga ruwa marar tsafta.
Haka sanarwar ta ce za a iya ɗauka ko kamuwa da cutar abinci mai guba da sauran matsalolin da za su iya kawo illa ga lafiyar jama’a.
Kan haka ne sanarwar ta bayar da shawara cewa duk wanda zai sayi kayan miya to ya je wurin da ya amince ko kasuwar da ya yarda da ingancin kayan da ake sayarwa a can, kuma a tabbatar an wanke sosai.
A wannan mawuyacin hali da jama’a ke ciki a Maiduguri, ma’aikatar ta roƙi mutane su bai wa kula da lafiyar su matuƙar muhimmanci.
