Sojoji sun kashe ‘yan fashin daji tare da kuɓutar da mutane 20 a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sojoji sun kashe ‘yan fashin daji 4 tare da kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su guda 20 a wani farmaki na kwanaki biyu da suka kai a Birnin Gwari da ƙaramar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Samuel Aruwan, wanda ke riƙon muƙamin kwamishinan ma’aikatar tsaro ta cikin gida na jihar Kaduna, ya yi bayanin cewa sojojin na rundunar tsaftace daji sun yi aikin su a Alawa na ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

Rahotanni sun ce sojojin sun hangi giftawar ‘yan fashin dajin a kusa da Kwaga, inda daga bisani suka hallaka biyu daga cikinsu tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da babura uku.

A wani rahoton kuma,  sojojin shiyya na 6 da suke aikin sintiri a Nakwakina dake karamar hukumar Giwa sun samu bayanan sirri inda suka afkawa ‘yan fashin daji.

Farmakin na sojojin ya haifar da rasa rai na ‘yan ta’addan guda biyu yayin da wasu suka gudu da raunika na bindiga. Sojojin sun ƙwato motoci guda 2 da wayar hannu.

Bugu da ƙari, sojojin na shiyya ta 3 sun samun kiran waya kan harin ‘yan fashin dajin inda suka isa wurin suka kama su a Polewire.

Rahotanni sun ce ‘yan fashin dajin sun tsere yayin da suka hangi sojojin waɗanda suka ceto mutane 20 da aka sace tare da miƙa su ga iyalansu.

Gwamna Uba Sani ya bayyana gamsuwa da rahotan inda ya godewa hukumomin tsaro.

Ya yaba wa Manjo Janar MLD Saraso wanda ke jagorantar runduna ta 1 ta sojin Nijeriya bisa nasarar da suka samu a Birnin Gwari da Giwa.

Gwamnan ya buƙaci sojojin da su ci gaba da nuna ƙwazo wajen yaƙi da ‘yan fashin dajin.

By ukarofi