Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribaɗu ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan ƙudurin dokar kafa cibiyar kula da ƙananan makamai ta ƙasa.
Ribadu ya bayyana haka ne a wajen taron ƙarawa juna sani kan hana yaɗuwar ƙananan makamai a Nijeriya da kuma yankin yammacin Afirka a ranar Talata a Abuja.
Ya ce hakan zai ƙara wa cibiyar ƙwarin guiwa wajen gudanar da ayyukanta.
A jawabinsa na buɗe taron, kodinetan hukumar NCCSALW na ƙasa DIG Johnson Kokumo mai ritaya, ya ce cibiyar a ‘yan kwanakin nan, ta samu wasu muhimman nasarori a yaƙi da yaɗuwar ƙananan makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Kokumo ya ce, a ranar 1 ga watan Yuli, cibiyar ta kwato wasu tarin haramtattun makamai daga hukumar kwastom ta Nijeriya, daga bisani kuma ta kama wasu mutane 10 da ake zargi da hannu wajen shigo da su ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce a halin yanzu hukumar NCCSALW tana tuhumar waɗanda ake zargi da shigo da su Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba, da kayayyakin da aka haramta – Bindigogi 544 da harsasai 112,500 wanda ya saɓa wa sashe na 3 (6) na Dokar Laifukan Mabambantan Cap M17 na Tarayyar Nijeriya 2004 da dai sauransu.
Cibiyar Yaƙi da ƙananan Makamai ta ƙasa (NCCSALW) ce ta shirya taron bitar.
Darakta Ibrahim Babani ne ya wakilci Ribaɗu a wurin taron.
