Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Bayan rantsar da shugabanin ƙungiyar Injiniyoyin ta Nijeriya NSE reshen Jihar Kano, wato Nigirians Sociaty of Engeers wanda aka zaɓa ta hanyar maslaha da gajeruwar muhawara wacce daga bisani aka amince da Eng Murtala Alhaji Garba a matsayin shugaban NES da zai ja ragamar ƙungiyar na shekara biyu da sauran mataimakansa da su ma aka yi maslahar amincewa da su a muƙamai daban-daban na shugabancin NES Kano a ranar Larabar da ta gabata.
A lokacin da yake jawabinsa a karon farko, Injiniya Murtala ya nemi haɗin kan ɗaukacin shugabannin NES na yanzu da waɗanda suka gabata da sauran “yan ƙungyar ta hanyar ba da shawarwarwari domin samun nassarar NES.
Tun da farko ya ce babban burinsa shi ne kammala ginin shalƙwatar ƙungiyar na dindindin da aka fara bai kammlu ba har yanzu, ya kuma yaba wa Egn Ibrahim Usman Dederi, tsohon shugaban ƙungiyar mai barin gado kan nasarorin da ya samu musamman wajen ƙwarin gwiwar ‘yan ƙungiyar da ɗaga darajarsu a Kano da ma Nijriya baki ɗaya.
Tuni dai Eng Murtala ya kama aiki bayan karɓar ragamar shugabanci daga Eng Dederi tsohon Shugaban NSE na Kano.
