An buƙaci gwamnati ta tallafa wa ’yan ƙungiyar masu facin tayu a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a  Lafiya

An yi kira na musamman ga gwamnatoci a dukka matakai a Jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya, su riƙa tallafa wa ’Yan ƙungiyar Masu Facin Tayu da ake kira ‘Association of Fucknizers in Nigeria’ a Turance na ƙasa, reshin jihar da kayayyakin aiki don ba su damar dogara da kansu.

Shugaban ƙungiyar a jihar, Alhaji Salisu Usman ne ya yi wannan kira a jawabinsa a wajen wani babban taron ƙungiyar na wata-wata wanda aka gudanar a Lafiya babban birnin jihar a karshen mako daya gabata. 

Ya ce, a halin yanzu akwai ’ya’yan ƙungiyar da dama a jihar da suka kammala koyon sana’ar ta facin tayu sai dai har yanzu basu da kayayyakin da zasu fara gudanar da nasu aikin duk da sun kware sosai a sana’ar.

Alhaji Salisu Usman ya bayyana cewa, ƙungiyar tana cigaba da ba da gagarumin gudumawa wajen cigaban jihar da ƙasa baki daya ta sana’arta.

Shugaban ya kuma buƙaci gwamnatoti a duka matakai su samar wa ƙungiyar da ababen hawa musamman mota don inganta harkokin su a jihar kasancewar a yanzu haka suna fuskantar matsalar rashin ababen hawan da hakan ke hana su tafiye-tafiye a ciki da wajen jihar.

Shima da yake sokaci, tsohon shugaban ƙungiyar a jihar ta Nasarawa wanda a yanzu shi ne babban sakataren shirye-shiryen ƙungiyar na ƙasa wato kwamrad Abdulra’aman Yakubu, ya buƙaci mambobin ƙungiyar su tabbatar suna bin dokokin ƙungiyar musamman atsalin ’yan gari. 

Abdulra’aman Yakubu ya kuma kira da a riƙa ɗaukar kwararan matakan hukunci ga duk mamban ƙungiyar da ya taka ɗaya daga cikin dokokin ƙungiyar don ya kasance darasi ga saura.

Sauran shugabannin ƙungiyar a matakai daban-daban da suka yi jawabi duk sun yi kira a cigaba da hada kai tsakanin mambobin a kuma cigaba da bai wa shugabanni cikakken goyon baya don kai ƙungiyar mataki nagaba.

By ukarofi