Ba zan sake goyon bayan Fubara ba har abada – Wike

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja Nyesom Wike, ya ce sha alwashin cewa ba zai sake goyon bayan Gwamna Fubara na Jihar Ribas ba, har abada.

Wike wanda tsohon gwamnan jihar Ribas ne wanda shi ya gama wa’adinsa Fubara ya maye gurbinsa, ya ce har abada babu sauran shiri ko sasanci tsakaninsa da Fubara.

“Ba zan taɓa sake goyon bayan Fubara ba a tafiyar siyasa, har ƙarshen rayuwa ta. Ba wai don Ni ba. Mutane sun sha wahala sun gina jam’iyya bisa tafiya mai tsari, amma wahalar ta zama ta banza,” haka Wike ya furta a tattaunawarsa da Gidan Talabijin na Channels, a ranar Juma’a.

Wike shi da kan sa ya zaɓi Fubara matsayin wanda zai gaje shi a zaɓen Gwamna na 2023, a ƙarƙashin PDP, Fubara ya yi nasara.

Ya ce ba don shi Wike ɗin ya jajirce lallai ko ana ha-maza-ha-mata ba, da ko na 50 Fubara ba zai zo a zaɓen ba, ballanata ya yi na ɗaya wanda ya yi nasara.

“Na yi sadaukarwa na yi ta magana da ‘yan ƙabilar Ogoni, na yi sadaukarwar shawo kan al’ummomin yankuna daban-daban, na yi magana da ɗaiɗaikun mutane dangane da yadda za mu kai Fubara ga nasara.

“Amma sharrin da ya fara yi min shi ne wai ina neman ya ba ni Naira biliyan 50, ya ba ni Naira biliyan 100. Ka ƙirƙiri ƙarairayi a kai na.

“Ni na ɗaga ka daga ba kowa ba har ka zama gwamna. Amma a yau ka yi min butulci, wai ni ina neman abin da ya fi ƙarfin ka ba ni daga hannun ka,” inji Wike.

Ya ci gaba da cewa Fubara bai gode masa shi da ya ɗora shi kan mulki ba, kuma bai nuna godiyar sakayya ga waɗanda suka taimaka har ya yi nasarar zama gwamna ba. Ya ce abin da kawai Fubara ya sa a gaba yanzu shi ne tarwatsawa da karya gadar siyasar da ya hau ya zama gwamna.

“Kai da a baya ba a bakin komai ka ke ba. Ka zama wata tsiya a dalilin ɗaga ka sama da wani ya yi. To don me za ka ƙaryata haka? Ai wannan rashin adalci ne a gare ni. Kuma wai sai ka yi tunanin na zauna haka kawai na zura masa ido?” Inji Minista Wike.

Da aka tambayi Wike abin da ya nema wajen Fubara, cewa ya yi, “abin da kawai na nema shi ne na ce masa kada ya watsar da waɗanda suka sha wahalar kai shi matsayin da ya ke a kai.”

By ukarofi